in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Michel Platini Na Son Sauya Matsayin Gasar UEFA
2013-11-29 16:03:07 cri


A yau za mu dan yi duba ne kan shugaban hukumar wasan kwallon kafar nahiyar Turai UEFA, kuma tsohon dan wasan kwallon kasar Faransa wato Michel Platini. Wanda a kwanan baya, jaridar "The Independent" ta kasar Birtaniya, ta watsa wani labari a kan sa, wanda ya baiwa masu sha'awar wasan kwallon kafa dake sassan wannan duniya daban daban matukar mamaki.

An ce dai Michel Platini na son mai da gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar 2020 ne ta zama wata 'karamar gasar cin kofin duniya', ganin yadda ake shirin gayyatar wasu kungiyoyin kasashen dake wajen nahiyar Turai, kamarsu Argentina, Brazil, Mexico, da Japan domin halartar gasar ta UEFA.

Wannan labari tilas ya ba jama'a mamaki matuka, ganin yadda wannan kuduri ka iya kawo babban sauyi ga tsarin da aka saba da shi. Sai dai wannan tunani ya kasance daya daga cikin gyare-gyaren da mista Platini ke shirin aiwatarwa, baya ga yawancin ragowar gyare-gyaren da za su shafi tsarin gudanar da gasar cin kofin nahiyar ta Turai. Ga misali, zuwa lokacin gasar da za ta gudana a shekarar 2016, za a sanya kungiyoyi 24 a maimakon guda 16 na yanzu shiga wasannin zagayen karshe.

An ce hukumomin wasan kwallon kafa na yankunan Scotland da Ireland ne suka fara mika rokonsu, na sanya karin kungiyoyi shiga gasar a shekarar 2007. Daga bisani, Platini wanda ba da jimawa ba ya zama shugaban hukumar ta UEFA a lokacin, ya amince da rokon wadannan kasashe. Sa'an nan a shekarar 2008, majalisar zartaswa ta UEFA ta zartas da shirin, inda ta sanar da kara shigo da wasu kungiyoyi 8 a gasar dake tafe a shekarar 2016.

A da kungiyoyi 16 ne ke halartar gasar cin kofin nahiyar Turai, wadanda a kan zabo su daga rukunai 4, kana baki daya a kan yi wasanni 31. Bayan canza wannan tsari, ana sa ran a shekarar 2016, gaba daya kungiyoyi 24 ne za su shiga gasar, wadanda za su fito daga rukunai 6, kana za su gudanar da wasanni 51 baki daya. Ta wannan sabon tsari ana fatan ganin an kara janyo hankalin masu kallon wasannin na kwallon kafa.

Idan an ce Platini ya kara yawan kungiyoyi masu halartar gasar cin kofin nahiyar Turai bisa sauraron shawarar da aka ba shi, a hannu guda ana iya cewa kuma sanya kasashe 13 karbar bakuncin gasar cin kofin na Turai a shekarar 2020 ra'ayin sa ne na kashin kansa.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China