in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Michel Platini Na Son Sauya Matsayin Gasar UEFA
2013-11-29 16:03:07 cri

A watan Janairun shekarar 2013, majalisar zartaswa ta hukumar UEFA ta zartas da cewa, za a gudanar da gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2020 a birane 13 na kasashe 13 dake nahiyar. Hakan ya dace da burin Platini na yada tsarin gasar cin kofin zakarun Turan.

Yanzu haka dai birane 39, daga kasashe 32 ne ke neman karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turan. Kuma daga karshe hukumar UEFA za ta zabi 13 daga cikinsu, ta kuma sanar da sunayensu a watan Satumban shekarar 2014 dake tafe.

Dangane da kwaskwarimar da mista Platini zai yi wa gasar cin kofin nahiyar Turai, jaridar "the Independent" ta ce Platini zai yi kokarin sanya gasar ta zama tamkar 'karamar gasar cin kofin duniya'. Kamar yadda wani mashawarcinsa ya bayyana, cewa 'tun da a kan gayyaci baki daga ketare don halartar gasar cin kofin Amurka, to me zai hana a gayyaci wasu kasashe shiga gasar cin kofin na Turai?'

Idan muka waiwayi tarihi za mu ga lokacin da aka fara kaddamar da gasar cin kofin Amurka a shekarar 1993, an fara ne da buga wasa tsakanin kungiyoyin kasashen kudancin nahiyar Amurka kadai. Amma zuwa wannan lokaci, wasu kasashen dake wajen kudancin Amurkan kamarsu kasar Amurka, da Mexico, su ma sun taba halartar gasar. Kana kasar Japan dake nahiyar Asiya ita ma za ta halarci gasar a shekarar 2015.

Idan majalisar UEFA ta zartas da dokar shigar da kasashen sauran nahiyoyin duniya cikin gasarta, kungiyoyin da za su samu damar halarta, a cewar jaridar "The Independent", su ne kasar Brazil, da Argentina, da Mexico da kuma Japan, wato kasashen da suke da karfi a fannin kwallon kafa a nahiyoyinsu.

Idan muka sake duba kan batun nan na gyaranbawul da Michel Platini ke kokarin yi wa gasar cin kofin nahiyar Turai, ta hanyar kara yawan kungiyoyin da za su halarci gasar, da sanya karin birane karbar bakuncin gasar, gami da neman gayyatar kungiyoyi na sauran nahiyoyi don su shiga gasar, ta haka za mu iya fahimtar burin Platini na habaka tsarin gasar, da daukaka matsayinta a idon duniya.

Ma iya cewa yana kokarin neman yiwa gasar cin kofin duniyar kishiya ne, ta hanyar daga matsayin gasar ta UEFA, sai dai mista Sepp Blatter, shugaban hukumar wasan kwallon kafan duniya FIFA, ba zai son ganin hakan ba. Dalili kuwa shi ne, shi ma tuni ya dauki wasu matakai na rage tasirin da nahiyar ta Turai ke da shi a wannan fage. Ga misali, a da an sanya kungiyoyi 24 shiga gasar cin kofin duniya, wadanda 13 daga cikinsu kan zo daga nahiyar Turai. Amma daga bisani aka kara yawan kungiyoyin dake halartar gasar zuwa 32, ko da yake kuwa ba a kara yawan kasashen Turai dake cikinsu ba, har ya zuwa gasar da za a gudanar a Brazil a shekarar 2014, kungiyoyin kasashen Turai 13 ne za su halarci gasar.

Wani ma abin lura shi ne, duk da cewa kuloflikan nahiyar Turai na da karfi, amma hukumar FIFA ta fi samun kudi daga nahiyar Asiya, wanda ya kai rabin kudin shigarta, yayin da kudin da kasashen Turai suke samarwa bai wuce kaso 20 kacal ba. Don haka ne ma Blatter ya taba nuna fatan ganin kasashen Asiya sun samu karin kujeru a gasar cin kofin duniya.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China