in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen Sin da India su karfafa alakar da ke tsakaninsu.
2013-10-24 11:02:23 cri
A ranar 23 ga wata, a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na kasar India Manmohan Singh, inda bangarorin biyu suka cimma matsaya daya game da burin raya alakar da ke tsakaninsu, domin samar da ci gaba cikin hanzari a cikin sabon zamani.

Mr. Li ya ce, kasancewar kasashen biyu na makwabtaka da juna, baya ga kasancewar su manyan abokai a fannin hadin gwiwa, ya dace su mayar da bunkasuwar juna babbar dama da za su amfana, kuma su inganta hadin gwiwa da samun ci gaba tare. Hakan ba wai kawai zai iya samarwa al'ummar kasashen biyu da yawansu ya kai biliyan 2.5 yanayin jin dadin rayuwa ba ne, a'a yana ma iya haifar da babban tasiri ga kasashen dake Asiya, da ma duk duniya baki daya.

Kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar India, don karfafa aniyar inganta alakar da ke tsakaninsu, ciki har da karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro bisa manyan tsare-tsare, da kara raya makomar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da inganta hadin gwiwa wajen kafa yankunan raya sana'o'i a tsakanin bangarorin biyu. Sauran sassan sun hada da inganta muhimman ababen more rayuwa, ciki har da gina hanyoyin jiragen kasa, da kafa kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen Sin, India, Myanmar, da Bangladesh, da yin amfani da damar shekarar sada zumunta, da yin mu'amala tsakanin kasashen biyu da aka kebe a shekarar 2014, don kara yin mu'amalar al'adu a tsakaninsu.

Har ila yau, Li Keqiang ya ce ya zama wajibi bangarorin biyu su kawar da sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar da ta dace, su kuma gudanar da taron tattaunawa na musamman, don gane da tsaron iyakokin kasashen biyu, da lalubo bakin zaren warware batutuwan da bangarorin biyu ke tattaunawa a kan su, tare da inganta hadin gwiwa a fannoni da dama.

A nasa bangare, Singh ya ce, sada zumuncin dake tsakanin kasar sa da Sin, wata babbar manufar diplomasiyya ce, kuma India tana fatan raya dangantakar bangarorin biyu ta fannonin amincewa da juna ta fuskar siyasa, da yalwata moriyar juna, da sa kaimi ga karfafa fahimtar juna, don ci gaba da raya hakikanin hadin gwiwar kasashen biyu, da kuma tabbatar da zaman lafiya da lumana a shiyya-shiyya da kuma dukkanin fadin duniya baki daya.

Bayan shawarwarin, firaministocin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 9 da suka shafi bunkasa sufuri, da makamashi, da tsaro, da al'adu, da ilmi, da kuma mu'amala a tsakanin kananan hukumomi. Har ila yau sun gana da wakilan shugabannin masana'antu na kasashen biyu. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China