A bayanin da likitocin da suka duba ta suka bayar sun ce ta cika ne da misalin karfe 2 da 15 na safiya agogon India a asibitin Mount Elizabeth dake Singapore kusan makwanni biyu bayan da ta gamu da wannan mummunan aiki na fyaden gamayya da wassu maza su shidda suka yi mata a cikin motar bas da ta shiga abin da ya firgita 'yan kasar na Indiya matuka ya kuma jawo zanga zangar nuna takaicin faruwar hakan a babban birnin kasar, kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwar dan sanda daya.
Budurwar wadda ke karatun aikin likita a jami'ar Delhi an kaita wani asibiti a kasar Singapore ne cikin jirgin saman daukan marasa lafiya a ranar Alhamis bayan da aka yi mata a kalla aikin fida iri uku a wani asibitin gwamnati dake babban birnin kasar India wato New Delhi.
Firaministan kasar Indiya Manmohan Singh ya jagoranci masu nuna jajen su tare da mika ta'aziya game da rasuwar budurwar yana mai ba da tabbacin cewa za'a dauki dukkan matakin da ya kamata na kare mata a kowane matsayi, sannan kuma ya bukaci jama'a masu zanga zanga da su kwantar da hankalinsu tare da karkata juyayinsu ta hanyar da zai ba da ma'ana cikin lumana.
Ita dai wanna budurwa a ranar 16 ga watan nan ne wassu maza 6 suka mata fyaden gamayya tare da mata dukan fitar arziki, sannan suka jefo ta waje daga cikin motar bas din da suka shiga ita da saurayinta bayan sun fito kallon sinima da misalin karfe 9.30 agogon Indiya kuma daman tun da suka shiga diraban motar bai tsaya ba.
Dukkan mazan da ake zargi dai an kama su kuma yanzu haka suna tsare a gidan maza suna sauraron karar da za'a shigar a kan su a mako mai zuwa. Wassu manyan jami'an 'yan sanda biyu suma an dakatar da su bisa zargin ba su ba da taimakon da ya kamata ba wajen hana aukuwar wannan aika aika. (Fatimah Jibril)