Taken taron shi ne "kasashe membobin kungiyar BRICS suna kokarin raya dangantakar abokantaka a fannonin samun zaman lafiya da wadata". A gun taron, Hu Jintao zai bayyana matsayin kasar Sin game da batutuwan kula da harkokin duniya, samun bunkasuwa mai dorewa, hadin gwiwa a tsakanin kasashe membobin kungiyar BRICS da dai sauransu. Bayan taron, za a bayar da sanarwar Delhi.
Yayin da ake gudanar da taron, Hu Jintao zai gana da shugabannin kasashe da abin ya shafa.(Zainab)