Kungiyar UNESCO ta ce, an shirya wannan aikin gwaji ne ta hanyar kwaikwayon bala'in igiyar ruwa da ya abku a ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 2004, a wancan lokaci, girgizar kasa da karfinta ya kai ga matsayi na 9 bisa ma'aunin Richter ta auku ne a gabar kogin tsibirin Sumatra dake kasar Indonesiya, sa'an nan ta haifar da bala'in igiyar ruwa, kuma igiyar ruwa ta ratsa tekun Indian cikin awoyi 12, kuma ta kai gabar tekun da ke kudancin kasashen Afrika.
Kungiyar UNESCO ta ce, mukasudin aikin gwajin shi ne don a tabbatar da shirin aikin ko ta kwana game da rage asarar da za a samu sakamakon bala'in igiyar ruwa a tekun Indian, da tabbatar da harkokin sadarwa tsakanin bangarorin da abin ya shafa, da tabbatar da matakan gaggawa da kasashen da abin ya shafa za su dauka, kana da tabbatar da karfin kasashen da ke gabar tekun Indian wajen kaurata da mutane.(Bako)