in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna matukar bakin ciki kan rasuwar wata budurwa 'yar Indiya da aka yi wa fyade
2012-12-30 16:28:23 cri
A daren ranar 29 ga wata, ta hannun kakakinsa ne Ban Ki-moon, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ba da wata sanarwa, inda ya nuna matukar bakin ciki kan rasuwar wata budurwa 'yar kasar Indiya da wasu gungun maza suka yi mata fyade, sa'an nan ya kalubalanci gwamnatin Indiya da ta kara daukar matakan hana sake abkuwar irin wannan danyen aiki.

A cikin sanarwar da ya bayar, mista Ban ya nuna bakin cikinsa kwarai da gaske kan rasuwar budurwar nan 'yar shekara 23 da maza 6 suka yi mata fyade a cikin motar bas a birnin New Delhi, hedkwatar Indiya a ran 16 ga wata, tare da nuna jaje ga iyayenta, danginta da abokanta. Ya kuma yi tir da kakkausan murya kan irin wannan aika-aika na marasa tausayi. Mista Ban ya furta cewa, ko kadan ba a amince da azabtar da mata ba, ba za a yafe wa wadanda suka aikata wannan laifi ba, kuma ba za a yi hakuri kan irin wannan laifi ba. Ya zama tilas a girmama ko wace mace, tare da sanya muhimmanci kansu da ba su kariya.

Har wa yau mista Ban ya yi maraba da matakan da gwamnatin Indiya ta dauka cikin gaggawa, ya kuma kalubalance ta kara daukar matakai da kuma yin gyare-gyare domin hana sake abkuwar irin wannan al'amari, da kuma gurfanar da masu laifi a gaban kotu. Ya karfafa gwiwar gwamnatin Indiya da ta inganta matakai masu muhimmanci da ke bai wa wadanda aka yi musu fyade. Haka zalika Ban ya ce, hukumar kula da harkokin mata ta MDD da sauran hukumomin da abin ya shafa a shirye suke wajen ba da tallafin ilmi, fasaha da dai sauransu da gwamnatin Indiya ke bukata wajen yin gyare-gyaren. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China