in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara inganta hulda a tsakaninta da kasar India
2012-03-30 11:36:57 cri

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da firaministan kasar India Manmohan Singh a ran 29 ga wata a birnin New Delhi. Inda shugabannin kasashen biyu suka sanar da cewa, an mayar da shekarar 2012 a matsayin shekarar sada zumunta da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da India, kuma sun bayyana cewa, za a daga matsayin huldar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu bisa wannan zarafi.

Ban da haka kuma, shugaba Hu Jintao ya nuna yabo ga bunkasuwar hulda a tsakanin kasashen Sin da India a 'yan shekarun da suka gabata, ya kuma jaddada cewa, a matsayin kasashe biyu masu tasowa kuma mafi girma a duniya kuma manyan kasashen biyu na Asiya, kasashen biyu suna da kyakkyawar damar neman samun bunkasuwa, kana suna da makoma mai kyau wajen raya huldarsu. Kasar Sin za ta nace ga sada zumunta da hadin gwiwa da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare da kasar India.

Manmohan Singh ya ce, hulda a tsakanin kasashen India da Sin ta zama daya daga cikin huldodin mafi muhimmanci a tsakanin kasa da kasa a karni na 21, kasar India ba za ta shiga tsarin hana bunkasuwar kasar Sin ba. Kasar India ta amince da jihar Tibet a matsayin wani cikakken yanki na kasar Sin, kuma ta nuna adawa ga duk wani yunkurin raba al'ummar kasar Sin da wasu 'yan kabilar Tibet dake zaune a kasar India suke kokarin yi. Kasar tana son kiyaye zaman lafiya a yankin iyakar kasashen biyu ta yadda za su daidaita batun iyakar kasa ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China