'Yan sandan kasar Indiya sun tabbatar a ran 21 ga wata cewa, an tada boma-bomai a jere a birnin Hyderabad, hedkwatar jihar Andhra Pradesh dake kudancin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 18 yayin da wasu sama da 50 suka jikkata.
'Yan sandan sun ce, an tada boma-bomai biyu da aka dana ne a kan babur guda 2 a wani wurin hada-hadar kasuwanci mai yalwa, dake cibiyar birnin Hyderabad, da misali karfe 7 na dare. Yawancin mutanen da suka mutu dai fararen hula ne.
'Yan sandan kuma sun gano wani bom daban a kofar wata gada marar nisa daga wurin. Ya zuwa yanzu, babu wani, ko wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin aiwatar da wannan hari. Amma wasu manazarta lamarin na ganin cewa, akwai alaka tsakanin harin da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Mujahideen dake kasar.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Manomhan Singh ya yi tir da wannan harin ta'addanci. (Amina)