Kakakin kungiyar OPCW Michael Luhan ya ce, ya zuwa ranar 22 ga wata, kwararru na kungiyar sun yi bincike a wuraren tanadar makamai masu guba 18 daga cikin dukkansu 23 a kasar Siriya, sannan aka rufe duk muhimman nau'rori a wadannan wurare. Luhan ya ce, ana gudanar da aikin lalata makamai masu guba bisa shirin da aka tsara, bayan ranar 1 ga watan Nuwamba, Siriya ba za ta iya kera makamai masu guba ba. Kungiyar OPCW tana da kwararru 27 a kasar Siriya, sannan akwai guda da yake kasar Lebanon.
Haka kuma, inji kakakin kungiyar an kafa rukunonin kwararru guda 3 don su iya gudanar da aikinsu, ya zuwa yanzu, an gudanar da aiki yadda ya kamata. Amma, kwararru na kungiyar ba su je yankunan da bangaren 'yan adawa ke mamaye ba don gudanar da bincike ba.
Michael Luhan ya ce, an samu hadin gwiwa tsakanin kungiyar da M.D.D. yadda ya kamata, kuma kasar Siriya ita ma tana bada hadin gwiwa yadda ya kamata. Bisa shawarar da kungiyar OPCW ta yanke a ranar 27 ga watan Satumba, kasar Siriya za ta mika shirin lalata makamai masu guba na farko ga kungiyar OPCW kafin ranar 27 ga watan Oktoba.(Bako)