A ranar 15 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana maraba da cimma yarjejeniya kan makamai masu guba na kasar Siriya tsakanin kasashen Amurka da Rasha. Kasar Sin tana fatan karfafa aikin warware matsalar Siriya ciki har da lalata makamai masu guba a karkashin jagorancin M.D.D tare da nuna cewa, ya kamata kwamitin sulhu na M.D.D. ya taka rawar a zo a gani game da batun.
A ranar 15 ga wata, yayin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ke ganawa da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewa, idan Siriya ba ta rushe makamanta masu guba kwata-kwata ba, to daukar matakin soja na Amurka na wurinta.
A sa'i daya kuma, a ranar 15 ga wata da dare, shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da tsayawa kan shirin daukar matakan soja ga kasar Siriya, a cikin shirin da kwamitin sulhu na M.D.D. zai zartas a mako mai zuwa, kamata ya yi a tsara shiri cewa, idan Siriya ba ta bi yarjejeniyar ba, to zata fuskanci takunkumin kasa da kasa.
A ranar 15 ga wata, ofishin kakakin sakatare janar na M.D.D. ya fada wa kafofin yada labaru cewa, a wannan rana, rukunin binciken makaman Siriya masu guba na M.D.D. ya mika rahoto ga sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-moon, kuma a ran 16 ga wata da safe Ban Ki-moon zai gabatar da wannan rahoto ga kasashe mambobin M.D.D. A sa'i daya kuma, mista Ban zai bayyana wa mambobin kwamitin sulhu wannan rahoto a lokacin ganawa ta sirri da ya yi tare da su, daga bisani kuma ya gana da manema labaru.(Bako)