Tawagar ta isa Siriya a ranar Talata domin soma wani aikin mai sarkakiya na bincike da tattara makamai masu guba a kasar Siriya da aka kiyasta yawansu zuwa tan dubu daya.
Kwamitin tsaro na MDD ya bada umurni ga kungiyar hana yaduwar makamai masu guda da ta taimakawa Siriya wajen lalata makamanta masu guba nan da tsakiyar shekarar 2014. Wadannan kwararru za su kwashe kimanin watanni tara domin kammala aikinsu. (Maman Ada)