A cikin sanarwar da ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar ta Rasha ta bayar, an ce, kwamitin sulhu na M.D.D. ya zartas da kuduri ne bisa tushen yarjejeniyar da kasashen Amurka da Rasha suka daddale tsakaninsu a tsakiyar watan Satumba, don sanya gwamnatin Siriya da ta shiga cikin yarjejeniyar hana yaduwar makamai masu guba, don tabbatar da gudanar da wannan aiki dake karkashin shugabancin M.D.D.
Haka kuma, ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar ta kuma bayyana cewa, bisa abubuwan da ke kunshe cikin yarjejeniyar, da gwamnatin Siriya da bangaren 'yan adawa, ya kamata su hada gwiwa da kungiyar hana yaduwar makamai masu guba ta duniya da M.D.D.
A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov a zantawarsa da kafofin yada labaru na kasar Rasha, ya bayyana cewa, kudurin da kwamitin sulhu na M.D.D. ya zartas da shi, bai kunshi daukar matakan soji ga kasar siriya ba. Bisa shirin kuduri, an ce, muddin dai ba a aiwatar da yarjejeniyar ba, kuma an tabbatar da cewa, Siriya ba ta aiwatar da yarjejeniyar ba, kwamitin sulhu na M.D.D. zai iya zartas da wani sabon kuduri bisa abubuwan da ke kunshe cikin kundin tsarin mulki na M.D.D., wanda zai iya shafar daukar matakan soji don kawo zaman lafiya da karko.(Bako)