Zaunannun kasashe 5 a kwamitin sulhu na M.D.D. sun cimma matsaya kan kudurin da ya shafi makamai masu guba a Siriya
A ranar 26 ga wata da yamma, zaunannen wakilai a kwamitin sulhu na MDD na kasar Amurka Samantha Power da na kasar Birtaniya Mark Iyall Grant sun fitar da bayani ta shafin Internet dinsu cewa, kasashe 5 da ke da kujeru din-din-din a kwamitin sulhu na M.D.D. sun cimma matsaya kan kudurin da ya shafi makamai masu guba a Siriya.
Madam Power ta kuma bayyana cewa, a wannan rana da dare za a mika daftarin shirin ga mambobi 15 na kwamitin sai dai ba ta fayyace abubuwan da ke kunshe a cikin daftarin ba.(Bako)