Majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa masanan sun gudanar da ayyukansu na farko a wasu wurare, amma ba tare da cikakken bayani ba a wuraren da suka je ba.
Haka kuma tashar talibijin ta kasar Lebannon Al-Manar ta rawaito cewa tawagar kwararrun da ta isa Siriya ta je ne domin taimakawa kasar Siriya lalata tarin makamanta masu guba kamar yadda sabon kudurin MDD ya tanada na kaddamar da shirin lalata wadannan makamai masu guba na Siriya.
Tawagar dai na kunshe da kwararrun kungiyar hana yaduwar makamai masu guba (OIAC) da na MDD, in ji wata sanarwar da aka fitar a makon da ya gabata dake bayyana cewa tawagar ta samu ci gaba da kwarin gwiwa a ayyukan da ta fara a Siriya.
Tawagar kwararrun ta isa kasar Siriya a ranar Talata tare da kuma samun tattaunawa tare da manyan jami'an ofishin ministan harkokin wajen kasar Siriya kafin su dukufa wajen fara aikinsu da ya shafi gudanar da bincike da gano kimanin tan dubu daya na makamai masu guba a kasar Siriya.
Kwamitin tsaro na MDD ya umurci kungiyar OIAC da ta taimakawa Siriya lalata tarin makamanta masu guba nan da tsakiyar shekarar 2014. Wannan zai baiwa kwararrun lokaci na tsawon watanni kimanin tara domin kammala aikinsu. (Maman Ada)