A lokacin ganawar,Wang Yi ya ce, ganin ba'a dade ba da kasashen Amurka da Rasha suka daddale yarjejeniya game da makamai masu guba na Siriya, kuma gwamnatin Siriya ta shiga cikin yarjejeniyar hana makamai masu guba, tare da gabatar da jerin sunayen makamai masu guba nata da amincewa da a lalata su, hakan ya bada damar warware batun.
Don haka Mr Wang ya jaddada cewa, ya kamata a mayar da aikin lalata makamai masu guba da warware rikicin kasar ta hanyar siyasa.
A nashi bangaren Mr Brahimi ya nuna godiya ga kasar Sin da goyon baya da ta nuna ma yunkurin daidaita batun Siriyan yana mai cewa wannan abin a yaba ma kasar Sin ne.(Bako)