130823-shugaban-kasar-Zimbabwe-Bako.m4a
|
A ranar 22 ga wata, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da ya lashe babban zaben kasar, ya yi rantsuwar kaman aiki, don fara wa'adinsa na shugaban kasar karo na 6. A waje daya kuma, jama'ar kasar suna fata Zimbabwe za ta samu ci gaba cikin zaman lafiya, bayan da aka samu rikici a kasar.
A ranar 22 ga wata, a babban filin wasan kasar Zimbabwe, mutane da dama sun taru, kuma suna farin ciki sosai, jama'ar da yawansu ya kai sama da dubu 60 sun yi ta raye-raye da wake-wake, kuma sun gane ma idanunsu bikin rantsuwar kama aiki na shugaban kasar tare da manyan baki daga kasashe daban daban.
Da tsakar wannan rana, yayin da motar shugaba Mugabe da matarsa ta shigo babban filin wasan, jama'a sun yi musu maraba, kuma sun yi masa jinjina. Sa'an nan kuma, a karkashin shugabancin babban alkali na kasar, Shugaban kasar Robert Mugabe ya yi rantsuwar kama aiki. Ya ce, "A matsayina na shugaban kasar Zimbabwe, zan yi kokari don bautawa kasata da kuma mutunta tsarin mulkin da dokoki, zan yi kokari don kawo alheri ga kasata da jama'a."