A wannan rana, yayin da Lew ke zantawa da kafar yada labarai ta kasar Amurka NBC, ya ce, a cikin makwanni da dama da suka gabata, rikicin siyasa ne ya kawo tangal-tangal, ba rikicin tattalin arziki ba. Halin kunci da harkokin kudi ke ciki, ya kawo tsaiko game da tattalin arzikin kasar, amma ya yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Amurka zai farfado.
Lew ya ce, matsalar bashi da halin kunci game da harkokin kudin kasar Amurka ke ciki ya haddasa yawan bashin da kasar Amurka take bi cikin kankanin lokaci ya hau, kuma rufe wasu ma'aikatun gwamnatin Amurka ya kawo hasara da dama, amma an kasa tantance wadannan hasarar a yanzu, jama'a za su ci gaba da lura da alkaluman tattalin arziki cikin wani lokaci mai zuwa, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne a kauce wa takarar da ke tsakanin jam'iyyu biyu na kasar, don magance sake aukuwar irin lamari.(Bako)