Lokacin da yake bayani ta kafar talabijin din kasar ABC a shirinta na ''This week'', John Boehner ya ce babu wata kuri'ar amincewa a majalisar na kaucewa wannan shiri duk da cewar wassu 'yan jam'iayr ta Republican sun nuna sha'awar mara wa 'yan jam'iyyar Democrats na Shugaba Obama baya wajen zartar da dokar da za ta dakatar da rufe wasu hukumomin gwamnatin.
Ya dage ga bukatar ganin har sai Shugaba Obama da 'yan majalisar Democrats sun amince an tattauna, yana mai bayanin cewa majalissar ba za ta aiwatar da dokar ba ba tare da sharadin hana karuwar bashi ba, yana mai bayyana cewa ba zai so ya ga Amurka ta samu tabo wajen cimma biyan basukanta ba sai dai kuma ba zai kara matsayin adadin basukan da za'a iya karba ba har sai an tattauna sosai a kan yadda za'a shawo kan al'ammarin da ke kawo a ciwo bashin.
Ya ce matsayin bashin kasar yana cikin hadari saboda Obama ya ki yarda a zauna a tattauna, su kuma 'yan majalissar suna bukatar a tattauana ne domin gano yadda za'a iya bude hukumomin gwamnatin da kuma yadda za'a iya biyan kudaden, ammam duk wannan sai an fara tattaunawa..
Tun da farko dai Shugaba Obama ya bukaci 'yan majalissar da su amince a sake bude hukumomin gwamnati a kuma kara matsayin basukan da za'a iya karba ba tare da wani sharadi ba, yana mai jaddada a taron ranar Laraban da ta gabata da ya yi da 'yan majalaissar cewa ba zai tattauna game da matsayin basukan ba. (Fatimah Jibril)