Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta tabbatar a ran 11 ga wata cewa, a cikin wani mataki da sojojin Amurka suka dauka, sun kama wani babban jigon kungiyar Taliban ta Pakistan.
Kakakin ma'aikatar ya ce, sojojin Amurka sun kama Latif Mehsud, wanda ta kira 'shugaban 'yan ta'adda' na kungiyar Taliban dake Pakistan, kuma babban kamanda ne a kungiyar Taliban ta Pakistan, kana na hannun daman shugaban kungiyar Hakimullah Mehsud.
Kakakin ya ci gaba da cewa, kungiyar Taliban ta Pakistan ta sanar da daukar alhakin shirya makircin tada boma-bomai a dandalin Times Square da ke New York a shekarar 2010, da kuma jerin hare-haren da aka kai wa ma'aikatan diplomasiyya na Amurka, haka kuma kungiyar ta lashi takwabin, kara kai farmaki kan kasar Amurka.(Danladi)