An gudanar da taron ne a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, Jami'in kula da harkokin zamantakewar al'umma na kungiyar tarayyar kasashen Afirka ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun da suka gabata, an samu karuwar laifuffuka da ke da nasaba da miyagun kwayoyi a kasashen Somaliya, Kenya da kuma Tanzania.
Manyan dalilan da ya sa kungiyoyin da ke fataucin miyagun kwayoyi na kasa da kasa ke gudanar da ayyukansu a nahiyar su ne, gurbin da nahiyar take, da rashin aiwatar da dokoki dangane da haramta fataucin miyagun kwayoyi, Kana abin da ya fi tada hankulan jama'a shi ne, a halin yanzu masu fataucin miyagun kwayoyi sun hada kai da 'yan ta'adda, kamar a arewacin kasar Mali, kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi sun tattara kudi ta hanyar fataucin miyagun kwayoyi inda suka goyi bayan harin ta'addancin da suka kai.
Jami'in ya kuma bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu da kuma yin musayar ra'ayoyi don yaki da lafuffukan da suka shafi miyakun kwayoyi. (Maryam)