in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta zama mahadar sabbin hanyoyin fataucin hodar iblis a duniya
2013-10-16 10:22:02 cri

Yankunan yammaci da gabashin Afrika sun taso a matsayin wasu sabbin tasoshin jigila ga kungiyoyin dake amfani da jiragen ruwa masu daukar kwantena ko kananan kwale-kwale wajen fataucin miyagun kwayoyi dake fitowa daga yankin Latin Amurka ko yankin tsakiyar Asiya zuwa kasuwannin da za'a shigar da su, in ji wani jami'in kwamitin tarayyar Afrika. A yayin wani taron shiyya kan yaki da fataucin hodar iblis a birnin Harare, mista Olawale Maiyegun, darektan cibiyar harkokin jama'a na kwamitin ya bayyana cewa, Afrika tana cikin tsaka mai wuya dalilin girman iyakokinta da gabobinta da ba su da kariya, da kasashen da ba su da karfi tare da yin fama da yaki, sannan ga rashin tsarin shari'a mai inganci, cin hanci da rashawa da kuma sauran wasu kalubaloli na jama'a dake sanyawa nahiyar Afrika kasancewa wani dandalin fataucin miyagun kwayoyi.

A cewar ofishin MDD kan yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka, yawan hodar iblis da aka kama, musammun ma a shekarun baya bayan nan ya karu a kasar Najeriya, Benin, Togo da Tanzania.

Ofishin MDD shi ma ya bayyana cewa, a gabashin Afrika, yawan hodar ibils da aka kama ya karu da ninki goma daga shekarar 2009.

Haka kuma mista Maiyegun ya ce, yaki da barazanar fataucin kwayoyi na da matukar wuya, har ma ga kasashen da suka cigaba da zaman lafiya, domin haka ne Afrika take da bukata a halin yanzu da matakai masu karfi domin yaki da wannan matsala. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China