Dokar ta bayyana matakan da za a dauka don gyara halin mashaya kwayoyi, kamar yadda za gudanar da aikin kan wasu mutane bisa son ransu, da yadda za a iya aiwatar da aikin gyara hali a cikin unguwanni, da kebe mashaya kwayoyi domin a taimaka wajen gyara halinsu, gami da ci gaba da taimaka musu gyara hali bayan da suka dawo unguwanninsu. Kana dokar ta bayyana hukumomin da za su dauki nauyin wadannan matakai, da yadda za a aiwatar da aikin daidai ba tare da yin kuskure ba, da tsarin da zai tabbatar da cimma nasara, har ma ta fayyace hakkokin mashaya kwayoyi da abin da ya kamata su yi.
Dokar ta nuna kulawa sosai kan mutanen da za a taimakawa su gyara halinsu. Fannonin da ta kunsa kamarsu aikin gyara hali, da ba da jagoranci wajen samun farfadowar jikin mutum, da horar da mashaya kwayoyi don su iya wata sana'a, gami da ba da tallafi ga zaman rayuwarsu, dukkansu sun sheda yadda ake kokarin harhada albarkatun da za a iya samu daga al'ummar kasar, don taimakawa mashaya kwayoyi, ta yadda za su kara daukar rayuwarsu da muhimmanci, da barin yin amfani da miyagun kwayoyi, kana a karshe su koma rayuwa cikin al'umma. (Bello Wang)