Ban Ki-moon ya bayyana cewa, sumogar miyagun kwayoyi ta kawo barazana ga lafiyar jama'a da zaman lafiyar yankuna. Kasuwar sayar da miyagun kwayoyi ta kasar Afghanistan da take samun ribar dala biliyan 61 a kowace shekara tana samar da kudi ga masu tada zauna tsaye da 'yan ta'adda na duniya. Kana a yankin yammacin Afirka, cinikin hodar iblis a duniya ya kawo illa ga harkokin siyasa da zaman lafiya a kasashen yankin.
Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya ce, MDD ta kafa wani rukuni don tsara manufofi a kokarin kyautata hanyoyin yaki da miyagun kwayoyi da aikata miyagun laifuffuka a sakamakon shan miyagun kwayoyi.(Zainab)