Shugaban hukumar a jihar Abdullahi Abdul wanda ya sanar da hakan ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar a lokacin da yake bayanin nasarorin da hukumar ta samu a cikin wannan shekarar, ya ce, galibin kwayoyin da matasa suke amfani da shi a jihar wiwi ne da sauran kwayoyi masu saka maye.
A cewarsa, tuni mutane 51 tsakanin shekaru 18 zuwa 40 babban kotun gwamnatin tarayya ta yanke masu hukunci. sannan kuma akwai saura da suke jiran hukunci. Ya yi bayanin cewa, a cikin wannan lokacin an gyara rayuwar wassu mashayan su 69 da yanzu haka sun daina shaye shaye tare da komawa cikin 'yan uwansu.
Shugaban hukumar ta NDLEA a jihar Niger Abdullahi Abdul don haka ya yi kira ga iyaye, shugabannin addini da kuma masu fada a ji a cikin al'umma da su taimaka ma hukumar wajen wayar da kan jama'a domin a samu nasarar yaki da shan miyagun kwayoyi.(Fatimah Jibril)