Alkaluman kididdiga sun yi kiyasin cewa, kashi 15 cikin 100 na kudin shiga da kasar ke samu suna shigowa ne ta hanyar safarar miyagun kwayoyi, abun da ke nuna cewa, wannan bangare ya kasance wani bangare mai matsala. Safarar miyagun kwayoyi da aikin ta'addanci kan iyakoki na nakasa karfin dangantaka da zumunci tsakanin kasashe masu rauni, ya na kuma yin karen-tsaye ga dokoki tare da hana cimma muradin karni na MDD ta fannin ci gaba, cewar Ban Ki-moon a lokacin taron ministocin kasashe da suka amince da kudurin garin Paris kan gwagwarmayya da safarar miyagun kwayoyi da ake fitowa da su daga kasar Afghanistan.
Kokowa domin murkushe safarar miyagun kwayoyi shi ne za mu yi bakin kokarinmu, sabili da rage talauci da kuma kara bunkasa rayuwar al'umma, kamar yadda ya furuta a taron garin Vienna na kasar Austriya.(Abdou Halilou)