Ranar Talata 13 ga wannan wata a birnin Vienna na kasar Austria, wakilin kasar Sin a ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Vienna, Cheng Jingye ya jaddada cewa, Sin za ta nace ga daukar tsauraran matakan wajen yaki da miyagun kwayoyi ba tare da kasala ba.
A wannan rana a gun wani taron da MDD ta yi, Cheng Jingye ya yi jawabi da cewa, Sin na mai da hankali sosai kan yaki da miyagun kwayoyi tare da shirya wasu tsare-tsare masu amfani. Kuma Sin tana nacewa wajen warware wannan batu daga tushensa da rage yawan bukatar miyagun kwayoyi, tare da toshe hanyoyin samar da miyagun kwayoyi. Bugu da kari, Sin tana tsayawa kan hadin kai da kasashen duniya wajen gudanar da wasu ayyukan yaki da miyagun kwayoyi a duniya. Matakan da suka sa Sin ta samu ci gaban a-zo-a-gani a wannan fanni.
Cheng Jingye na ganin cewa, ya zuwa yanzu, matsalar miyagun kwayoyi tana yaduwa zuwa wurare daban-daban na duniya, hakan ya sa ake bukatar yin matukar kokari don neman kawar da wannan matsala.(Amina)