in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kira da bullo da matakan da za su kai ga samar da ci gaba mai dorewa
2013-09-18 10:47:17 cri

Babban sakataren MDD Ban ki-Moon, ya yi kira a ranar Talata yayin da babban zauren majalisar ke bude zamansa karo na 68 kan a kara himma wajen fito da matakan da za su kai ga samun ci gaba mai dorewa a shrekaru masu zuwa, sakamakon karewar irin ci gaban da aka samu a wannan zagaye.

Shekara ta 2015, ita ce zangon karshe na cimma manufofin muradun karni na MDGs, wato manufofin guda 8 na yaki da talauci da shugabannin kasashen duniya suka amince a taron kolin MDD a shekara ta 2000 wadanda suka bayyana manufofin kawar da talauci, samar da ilimi, samar da daidaiton jinsi, kula da lafiyar mata da kananan yara, kiyaye muhallai, rage yaduwar cutar kanjamau da hulda tsakanin kasa da kasa.

Ban Ki-moon ya ce, 'Za mu kara kokari wajen fassara ma'anar manufofin raya kasa da ake son cimmawa ya zuwa shekara ta 2015, ciki har da rukunin matakan maufofin da ake son cimmawa game da ci gaba mai dorewa da ake fatan zai magance tarin kalubalen da ake fuskanta a wannan zamani, kana a yi nazarin tunanin da ke zukatan al'ummar duniya, kamar yadda manufofin muradun karni wato MDGs suka yi nasarar hakan.

Ya kuma bayyana cewa, za a mayar da hankali kan hanzarta cimma manufofin muradun karni cikin kwanaki 1,000 kafin karewar wa'adin da aka tsayar.

Mr. Ban ya yi kira ga 'yan kasuwa, kungiyoyin fararen hula, masu hannu da shuni, da su taimaka wajen ganin an cimma nasarar muradun karnin, inda ya ce, MDD za ta mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya da kalubalen tsaron da ake fuskanta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China