A ranar Alhamis, kasar Sin ta yi kira ga hukumomi na kasa da kasa da a hada karfi domin magance talauci. Wanan abun zai hada da kirkiro wani yanayi mai kyau domin kawar da talauci ta hanyar daukar matakan rage talauci a cikin dukkan fasaloli na kasa, ta fannin tattalin arziki da ci gaban rayuwar al'umma, da girka wani gungun kan maganar rage lamarin talauci.
Wang Min, mataimakin wakilin Sin na din-din-din a MDD shi ne ya furta hakan a cikin jawabin da ya yi a wurin taro kan kawar da talauci da hukumar MDD mai kula da ci gaba da bunkasuwar rayuwar al'umma ta gudanar. Taron da aka bude a ranar Laraba a cibiyar MDD a garin New York, da kuma zai gudana a cikin kwanaki 10 .
Kokarin da kasashen duniya ya kamata su yi kan hanyoyin kawar da talauci na cikin kudurori guda 3 da jakadan kasar Sin ya gabatar.
Na farko, Wang ya ce, shi ne kokarin samar da wani yanayi na kasa da kasa mai nagarta wajen kawar da talauci. Cewar shi, idan babu yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, babu tabbas ga bunkasuwar tattalin arziki ke nan, babu wani matsayi kan maganar kawar da talauci.
Dukkan kasashe su tashi tsaye wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da darata juna a siyasance, da kokarin daidaita tattalin arziki da bunkasa shi ta yadda kowa zai samu nashi rabo daidai wa daida. Wang ya kara da cewa, mu darata kasashe a game da zabin da suka yi ta fannin hanyoyinsu na ci gaba da suka tabbatar ma jama'a.
Abun na biyu cewar Wang shi ne kawar da talauci tsari ne na dukkan tattalin arzikin kasa da ci gaban al'umma. Dukkan kasashe su debi girman lamarin ta hanyar fadada ayyuka, karfafa kare al'ummomi, da kare rukuni mai rauni, su ne hanyoyin kawar da talauci cewar Wang.
Na uku, gungun kasa da kasa sai ya yi kokari wajen kawar da talauci. Hukumomin kasa da kasa sai sun dauki maganar kawar da talauci da babban muhimmanci ta bangaren bunkasa hulda da kuma gano sabbin matakai da dubarori da kungiyoyi ya kamata su dauka wajen talafawa kawar da talauci.(Abdou Halilou).