in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta bayyana kudurinta na cimma manufofin muradun karni
2013-09-17 10:39:56 cri

A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta nanata kudurinta na ganin ta cimma manufofin muradun karni (MDGs) ya zuwa shekara ta 2015.

Wasu rahotanni sun ruwaito shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na bayyana hakan yayin taron kwamitin da shugaban kasa ya kafa game da sa-ido tare da kimanta manufofin muradun karni na MDGs wanda aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Mai taimakawa shugaban kasa ta musamman kan manufofin muradun karni, Precious Gbenol, ta bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta tallafa a bangarorin samar da kudi da yin hadin gwiwa a bangarori daban-daban.

Bugu da kari ta ce, gwamnatin za ta tabbatar da yin hadin gwiwa da jihohin kasar da zurfafa hadin gwiwa da abokan huldar kasa da kasa.

Gbenol ta ce, an cimma nasara a shekaru biyu da suka gabata a muhimman manufofi na farko, 3 da na shida, sannan akwai alamun da ke nuna cewa, za a cimma nasara a muhimman manufofi na 4, 5 da na 8.

Ta ce, a manufar farko, wadda ta mayar da hankali kan rage talauci, an cimma nasarar rage talauci daga kashi 19.3 cikin 100 zuwa kashi 8.25 cikin 100 a shekara ta 1991, sama da kashi 9.6 cikin 100 da ake son cimma wa zuwa shekara ta 2015. Ta kuma bayyana cewa, sun yi nasarar kawar da matsalar daidaito tsakanin jinsi da ake samu a makarantun firamare da sakandare. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China