Bisa labarin da aka samu ta shafin intanet na hukumar harkokin tsaron kasar Najeriya, an ce, za a kammala atisayen sojoji na tsawon lokaci makonni guda uku a ranar 24 ga wata. Ban da rundunar sojan kasar Najeriya, rundunonin sojojin tsaron teku da na musamman da suka zo daga kasashen Amurka, Burtaniya, Senegal, Ghana, Togo, Benin, Kamaru da sauran kasashe ne suka kuma halarci atisayen sojojin nan. Kuma abubuwan da aka yi yayin atisayen sojoji sun hada da dabarun yaki da 'yan fashin teku, kare filayen hako man fetur, da kuma yaki da yankunan koguna da dai sauransu.
Bisa labarin da rundunar sojan kasar Najeriya ta fitar, an ce, babban makasudin atisayen soja na wannan karo shi ne, a karfafa ayyukan kasashen Afirka dangane da samar da dabarun yaki da kuma gudanar da shirye-shiryen sojoji cikin hadin gwiwa a yankin teku, a sa'i daya kuma, ana fatan karfafa karfin sojojin kasar Najeriya wajen fuskantar kalubaloli a gabar teku na Guinea, musamman ma wajen fuskantar ayyukan satar man fetur da kuma kai wa jiragen ruwa na kasuwanci hari da 'yan fashin teku za su yi. (Maryam)