A ranar Alhamis, ministan cikin gidan Najeriya Abba Moro ya bayyana cewa daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Oktoba a matsayin ranakun biyu domin gudanar hidimar wannan salla.
Za'a jibge jami'an tsaro a muhimman wurare a cikin kasar da kuma gudanar da bincike kan motocin dake fice da shige a jihohin dake arewacin kasar. An kuma kara yawan jami'an tsaro a wasu jihohin kasar ta yadda jama'ar kasar za su yi bikin wannan salla cikin kwanciyar hankali da tsaro.
Wata majiyar tsaro a Najeriya ta shaidawa wakilin Xinhua cewa hukumomin kasar sun dauki matakan tsaron da suka wajaba a dukkan biranen kasar domin yin rigakafin duk wasu hare haren ta'addanci a lokacin sallar Aid el Kabir.
Sufeton 'yan sandar Najeriya, Mohammed Abubakar ya umarci hafsoshinsa na yankuna da na jihohi da su dauki matakan tsaro tare da bukatar manya manyan 'yan sanda na yankuna goma sha biyu na kasar da su karfafa yin sintiri da sanya ido, haka kuma ya kamata a baza 'yan sanda har zuwa wuraren shakatawa da muhimman wuraren jama'a dana gwamnati.
Haka kuma shugaban 'yan sanda ya bukaci kwamishinonin 'yan sanda na jihohin da su jibge ma'aikatan tsaro domin kiyaye zirga zirgar masu tafiye tafiye.
Abuja, babban birnin kasar, an kara karfafa matakan tsaro a ciki da kewayen birnin, haka kuma jami'an tsaro suna ko'ina a muhimman wurare tare da taimakon rundunar sojoji. (Maman Ada)