Babban sifeton rundunar 'yan sandan tarayyar Najeriya Mohammed Abubakar, ya bukaci jami'an rundunar da su kasance cikin shirin ko ta kwana, domin tabbatar da kammalar bukukuwan murnar samun 'yancin kan kasar cikin nasara.
Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labaru a Abuja, babban birnin tarayyar kasar, babban sifeton rundunar ta 'yan sanda ya umarci dukkanin manyan jami'an rundunar, da kwamishinoninta na jahohi, da masu tsaron iyakokin ruwa, da su tabbatar da tura isassun jami'ai dukkanin wuraren da suka dace, tare da samar da kyakkyawan tsarin gudanar da ayyukan tsaro.
Abubakar ya kuma yi kira gare su da su baiwa wuraren taruwar jama'a kulawar da ta dace, domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma.
Babban sifeton 'yan sandan ya kuma alkawarta baiwa al'ummar Najeriya dukkanin tsaron da ya wajaba, musamman ma a wannan lokaci na bukin tunawa da ranar samun 'yancin kan kasar karo na 53. Daga nan sai ya taya shugaban kasar Dr. Goodluck Jonathan murnar sake zagayowar wannan rana.
Bugu da kari, Abubakar ya bukaci 'yan Najeriya da su ajiye banbance-banbancen dake tsakaninsu gefe guda, su kuma hada kai tare da kara kwazo, wajen kawo karshen matsaloli, musamman ma na tsaro dake ci gaba da ciwa kasar tuwo a kwarya. (Saminu)