A jiya Alhamis 12 ga wata, kwamitin tsaro na MDD ya kara nuna damuwarsa game da halin fargaba da ake ciki a gabashin jamhuriyar demokradiya ta Kongo DRC, yana mai kira a samar da wata tsari da zai samar da hanyoyin kawo zaman lafiya a kasar.
A cikin wata sanarwa da Gary Quinlan, wakilin din din din na kasar Australia a majalissar wanda ke rike da shugabancin kwamitin a wannan wata na Satumaba ya ce, mambobin wannan kwamiti na nuna matukar damuwarsu.
Bayan sauraron bayani ta hoton bidiyo da Mary Robinson, manzon musamman a yankin Great Lakes, da kuma Martin Kobler, wakili na musamman na magatakardar MDD a jamhuriyar DRC suka yi, kwamitin ya yaba da ziyarar manzonin na musamman na kungiyar tarayyar kasashen Afrika, kungiyar tarayyar Turai da Amurka zuwa kasar, da ma Ruwanda da Uganda tsakanin ranar 3 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki domin karfafa zaman lafiya a yankin.
Haka kuma kwamitin ya goyi bayan aiwatar da yarjejeniyar dake karkashin shirin samar da zaman lafiya, tsaro, da hadin gwiwwa wajen samar da wani tsari ga kasar da ma yankin gaba daya wanda aka amince da shi a taron Addis Ababa na kasar Habasha da aka yi a watan Fabrairun wannan shekara. Yayin taron, kasashe 11 suka rattaba ma hannu a gaban magatakardar MDD Ban Ki-Moon da ya bukaci kasar ta DRC da ta zurfafa manufarta na samar da tsaro.
Kwamitin tsaron na MDD har ila yau yana zuba ido ya ga sakamakon taron da za'a yi a nan gaba game da yankin a ranar 23 ga watan nan da muke ciki a birnin New York. (Fatimah)