130925 bagwai correct.m4a
|
Matasa 386 ne cibiyar horas da dabarun sana`ar gadi da harkokin tsaro na zamani dake Karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano ta areawcin Najeriya ta yaye, a wani gagarimin biki da aka gudanar a ranar litinin din nan.
Wakilinmu dake Kano Garba Abdullahi Bagwai ya halarci bikin wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
Ita dai wannan cibiya na daya daga cikin manyan makarantu 20 da gwamnatin jihar Kano ta kafa a kokarinta na tabbatar da ganin matasa sun samu ayyukan yi, kuma wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da wannan biki cikin shekaru biyu.
Ya zuwa yanzu dai adadin matasa sama da dubu daya ne suka samu wannan horo, wanda ya ba su damar nakaltar dabarun zamani kan harkokin tsaro da kare kai.
Tuni irin wadannan matasa da suka samu horo a cibiyar suka samu damar samun ayyuka a ma`aikatu da hukumomin gwmanatin jihar Kano da kamfanoni masu zaman kansu da kuma wasu bankuna dake jihar.
Kwararru a kan harkokin tsaro sune suke tafiyar da cibiyar, kuma ana shafe watanni uku ne wajen bayar da horon, kana ana zabo matasan da ake horas wa ne daga yankunan kananan hukumomin jihar 44.
A jawabin da ya gabatar yayin bikin, gwamnan jihar kano Dr. Rabi`u Musa Kwankwaso yace gwmanatinsa ta dora mahimmancin gaske kan sha`anin tsaro, kuma zata samu cimma burinta akan haka ne kawai ta hanyar samar da aikin yi ga matasa.
Injiniyar Rabi`u Musa Kwankwaso ya bayyana gamsuwa kan yadda shirin bayar da horon yake tasiri ga yanayin zamantakewa da rayuwar matasan jihar ta Kano.
Gwamnan yace lokaci ya wuce da mutane zasu rinka daukar masu gadi marasa ilimi da kwarewa ta zamani.
Gwamnan jihar ta kano ya yaba bisa irin horon da matasan suka samu, musamman ganin yadda suka gudanar da fareti na musammam yayin bikin.
Injiniya Rabi`u Musa Kwnakwaso ya bayar da umarnin daukar wasu matasa 400 amma fa mata domin basu horo a wannan cibiya, kasancewar mata na da rawar takawa wajen tabbatar da samun ingantaccen tsaro a kasa.
Ya ce idan an kammala basu horo za a tura su makarantun mata da asibitocin jihar domin yin gadi da sauran ayyukan tsaro.
Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul`aziz Yari yana daga cikin bakin da suka samu damar halartar bikin, inda ya tabbatar da cewa a shekara mai zuwa jihar Zamfara zata turo matasanta zuwa wannan makaranta dake Kano domin samun horo.
Ya yaba bisa hangen nesan gwamnatin Kano na kirkiro da makarantar, lamarin da ya yace zai taimaka sosai wajen rage zaman kashe wando a tsakanin matasa
Ita dai wannan makaranta tana karkashin kulawar ofishin sakataren gwmanatin jihar Kano ne, kuma tana bayar da takardar shedar certificate da Diploma kan harkokin da suka shafi tsaro.(Garba Abdullahi Bagwai)