in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'amuran tsaro na kara tabarbarewa a arewacin kasar Mali
2013-09-30 10:30:50 cri

Wasu rahotanni daga kasar Mali na bayyana cewa, a wannan mako, al'amuran tsaro a arewacin kasar sun tabarbare, inda fada ya barke ranar Lahadi tsakanin 'yan tawayen Azbinawa (MNLA) da sojoji a yankin Kidal da kuma wani harin bam din kunar bakin wake da aka kai garin Timbuktu washe gari.

Mahukunta a yankin, sun bayar da rahoton musayar wuta a tsakiyar yankin Kidal, yankin da ya taba zama tungar 'yan tawayen na MNLA, amma daga bisani ya koma karkashin ikon sojojin kasar.

A ranar 18 ga watan Yuni ne, aka sanya hannun kan wata yarjejeniya a Ougadougou, babban birnin kasar Burkina Faso, tsakanin gwamnatin Mali da kungiyar kwatar 'yancin yankin Azawad (MNLA) da kungiyar hada kan yankin na Azawad (HCUA), wadda ta bayyana cewa, kamata ya yi a gudanar da tattaunawa tsakanin sassan don cimma zaman lafiya a kalla kwanaki 60 bayan zaben sabon shugaban kasa.

Ibrahim Boubacar Keita, wanda ya lashe zaben shugaban kasar a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Agusta, ya ayyana cewa, ba zai jira har kwanaki 60 din da aka tsai da na warware matsalar arewacin kasar ba.

Sai dai duk da yarjejeniyar da aka cimma, wani fada ya sake barkewa kwanaki bayan da bangarorin biyu suka gudanar da sabuwar tattaunawa, a wani kokari na kawo karshen duk wani abin da zai sake tayar da jijiyar wuya, lamarin da ya haddasa asarar rayuka a wasu fadace-fadace tsakanin sojojin kasar Mali da 'yan tawayen MNLA a wajen Kidal. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China