in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya ta yi alkawarin aiki tare da kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci
2013-10-11 10:41:18 cri

A ranar Alhamis 10 ga watan nan, gwamnatin kasar Somaliya ta ce, za ta hada kai tare da sauran kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci a kasar. dake kuryar Afrika.

Biyowa bayan zaman majalissar ministocin kasar, firaminista Abdi Farah Shirdon da ya jagoranci zaman ya ce, ministocin sun tattauna a kan samamen da sojojin Amurka suka yi a kan kungiyar Al-Shabaab a makon da ya gabata a garin dake bakin teku na Barawe na yankin Shabelle.

A cikin wata sanarwa, firaministan ya ce, gwamnatin Somaliya za ta hada kai da kasashen duniya wajen yaki tare da murkushe ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda wadanda suke jefa rayukan jama'a cikin wani mawuyacin hali, ba ma a kasar ba har ma nahiyar Afrika da duniya baki daya.

Sojojin Amurka sun kai wani samame na sanyin safiya a kan wani gidan da ake ganin kwamandan kungiyar Al-Shabaab ta kasar Kenya ke ciki domin su kamo wadanda ake zargi da kai hari a cibiyar kasuwancin na Westgate dake Nairobi a watan da ya gabata.

Gwamnatin kasar Somaliya ta ce, za ta ba da hadin kai wajen ganin an yi yaki da kungiyoyin ta'addanci domin hana su samun damar gina maboyansu a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China