Kasar Ghana da wasu kasashen Afrika na fama da wata babbar barazana daga kungiyoyin ta'adanci, matsalar da ya kamata a dauke ta da gaskiya, a cewar wani masanin harkokin tsaro a cikin wata hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Mataimakin darektan tawagar tarayyar Afrika (AU) a Laberiya, shehun malami Nii Nortey Addo ya bayyana cewa, wannan barazana ke iyar shafar kowace kasa, idan aka dubi hanyar da 'yan ta'addan ke bi wajen tafiyar da ayyukansu. Babu wata kasar za ta tsira domin 'yan ta'addan na daukar matakan kai hare-hare kan wasu kasashe da kadarorinsu.
Haka ne ya sa idan wata kungiyar ta'addanci na ganin wata kasa na gudanar da wasu ayyukan dake sabawa ka'idodinta, to wannan kasa da kadarorinta za su zama abubuwan kaiwa hari, in ji masanin na cibiyar tattaunawa da bincike kan harkokin tsaro a nahiyar Afrika (ASDR).
Da yake ba da misali kan harin boma-bomai na shekarar 1998 kan ofisoshin jakadancin kasar Amurka a kasashen Kenya da Tanzania, mista Addo ya nuna cewa, ko hukumar wakilcin wata kasa ba za ta tsira ba.
Ko da yake kasar Ghana ba ta da wani dalilin kasancewa cikin layin kasashen dake iyar fuskantar hari, amma ganin cewa, akwai ofisoshin jakadancin kasashen waje da kadarorinsu cikin kasar, hakan na iyar sanya 'yan kishin islama kaiwa kasar Ghana hari.
Wajibi ne kasar Ghana ta yi taka tsantsan da kuma daukar matakan tsaro da suka wajaba domin 'yan ta'adda na da wani salon yin amfani da mutane a cikin al'ummomi da kuma wuyar a gano su, balantana a dauki matakan yi rigakafi, in ji mista Addo. (Maman Ada)