in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci Amurka da ta fitar da sunanta daga jerin kasashen da ke mara wa ayyukan ta'addanci baya
2013-09-16 10:36:21 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA, ya bayar da rahoto a ranar Lahadi cewa, gwamnatin Sudan ta bukaci kasar Amurka, da ta fitar da sunan kasar daga jerin kasashen da ke daurewa ayyukan ta'addancin gindi.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Sudan ya ruwaito karamin sakatare a ma'aikatar harkokin wajen kasar Rahamtalla Mohamed Osman, yana cewa, kamata ya yi tun ba yau ba a fitar da sunan kasar daga jerin kasashen da Amurka ta zayyana a matsayin kasashen da ke mara wa ayyukan ta'addanci baya, domin a cewarsa, babu abin da ya hada kasar da ayyukan ta'addanci.

Osman wanda ya gana da manzon Amurka mai kula da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, Donald Booth a ranar Lahadi, ya bayyana cewa, kasar Sudan ba ta da wata alaka da ayyukan ta'addanci, don haka ya zama wajibi ga kasar Amurka ta sauke nauyin da ke kanta ta wannan bangare na cire Sudan din daga jerin wadannan kasashe.

Ya kara da cewa, gwamnatin Sudan tana jiran isowar sabon manzon Amurka domin ta gabatar da cikakken bayani game da wannan kuduri.

Jami'in ya ce, wasu mutane na ruruta batun yankin Abyei da nufin matsawa Sudan lamba, yana mai bayyana cewa, shugaba Omar al-Bashir na Sudan da takwaransa na Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit, sun tabbatar a yayin taron kolinsu da ya gabata kudurin sassan biyu na warware batutuwan da ke tsakaninsu ba tare da wani matsin lamba daga ketare ba.

Tun a shekara ta 1993 ne kasar Amurka ta sanya kasar ta Sudan cikin jerin kasashen da ke marawa ayyukan ta'addanci baya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China