Gwamnatin kasar Somaliya ta yi kira a ranar Litinin ga hadin kan shiyya domin dakatar da yawan barazanar kungiyoyin ta'adanci na shiyya-shiyya bayan harin da ya shafi wani babban shagon kasuwanci a Nairobi, babban birinin kasar Kenya.
Shugaban majalisar dokokin kasar Somaliya, Mohamed Osman Jawari ya bayyana cewa, harin cibiyar kasuwancin Westgate na nuna muhimmancin yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin wannan shiyya domin kawo zaman lafiya mai karko.
'Ya kamata mu yi aiki tare da kuma bullo da wata dabarar hadin gwiwa domin yaki da wannan annoba.' in ji mista Jawari a cikin wata sanarwa.
Kasar Kenya dai na fama da rashin tsaro daga watan Oktoban shekarar 2011, tun bayan da ta tura sojojinta zuwa kudancin Somaliya domin yaki da dakarun kungiyar Al-shabaab.
Sojojin Kenya sun je Somaliya ne domin tallafawa sojojin kasar wajen korar mayakan kungiyar Al-shabaab daga muhimmin sansaninsu na birnin Kismayo dake kudancin Somaliya da kuma wasu muhimman yankuna dake hannunsu.
Kenya na zargin gungun Al-shabaab dake da alaka da kungiyar AL-Qaida da ya hadasa rashin tsaro da sace masu yawon bude ido 'yan kasashen waje a kasar. (Maman Ada)