Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a jiya Lahadi ya ce, ba zai janye sojojin kasarsa daga Somaliya ba, ko da yake masu dauke da makamai na kungiyar Al-shabaab suke matsawa lamba ta hanyar kai hari a wani babban shago dake birnin Nairobi, inda fadar gwamnati take domin ramuwar gayya saboda sojojin da ya aika zuwa Somaliya.
Da yake jawabi yayin taron manema labarai na hadin gwiwwa da shugabannin 'yan adawa a Nairobi, Mr. Kenyatta ya ce, Kenya ba za ta yi kasa a gwiwwa ba a kokarinta na yaki da 'yan ta'adda a duk fadin duniya sakamakon daukan alhakin wannan harin babban shagon da kungiyar Al-shabaab ta yi.
A lokacin wannan taron da tsohon firaministan kasar Raila Odinga da tsohon mataimakin firaministan kasar Musalia Mudavadi suka rufa masa baya, Mr. Kenyatta ya yi bayanin cewa, a matsayin Kenya na kasa mai iko, ta tura sojoji a Somaliya ne domin yaki da ayyukan ta'addancin da ake aikatawa ga al'ummomin kasar ta Kenya, da ta Somaliya da ma sauran al'ummomi a kasashen duniya, don haka wannan ba yaki ba ne na kasar Kenya kadai, yaki ne na kasa da kasa.
Shugaban sai ya yi kira ga daukacin al'ummomi masu fatan alheri da su mara wa kasar baya, domin kara karfin yaki da ta'addanci tare.
Wannan furuci na shugaban kasar ya zama martani ga kalaman kakakin kungiyar Al-Shabaab wanda yake cewa, ko dai sojojin Kenya su fita daga kasar Somaliya, ko kuma kasar za ta dinga fuskantar hare-hare, a cikin shafinta na Twitter, kungiyar ta yi bayanin cewar, tuni ta yi gargadin cewar, za'a fuskanci martani idan har Kenya ta taimaka wa gwamnatin Somaliya wajen yakanta, saboda haka kashe-kashe a cikin wannan shago ramuwar gayya ce.
Sai dai shugaba Kenyatta ya yi watsi da barazanar kungiyar, yana mai cewa, za a rushe kungiyar nan ta ta'addanci ne cikin gajeren lokaci, kuma a wannan harin ne kawai 'yan ta'adda suka cimma buri domin sauran da suka kai ba su yi nasara ba. (Fatimah)