Mahukuntan kasar Somaliya sun bayyana amincewarsu da sakamakon babban taron kasa da kasa da aka gudanar, don gane da tsara yadda za a sake ginin kasar da yake-yake suka daidaita.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somaliyan ne ya bayyana matsayin kasar tasa, bayan da aka alkawarta samar da kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 2.4, wadanda za a yi amfani da su wajen sake ginin kasar.
Shugaba Hassan Sheikh, da jagorar sashen lura da harkokin kasashen ketare ta kungiyar tarayyar Turai Catherine Ashton ne dai suka jagoranci taron da ya gabata a birnin Brussels na kasar Belgium.
Da yake tsokaci don gane da wannan batu, faraministan kasar ta Somaliya Abdi Farah Shirdon, cewa ya yi, sakamakon taron na Brussels, tamkar wani ginshiki ne na sake ginin kasar bisa tsari mafi dacewa. Ya ce, shugabannin kasar sun sanya daukacin bangarorin masu ruwa da tsaki dake kasar, cikin shirin farfado da yanayin zaman lafiya.
Bugu da kari, Shirdon ya bayyana cewa, irin goyon bayan da Somaliyan ta samu, na nuni ga amincewar da kasashen duniya suka yi da ita, wajen iya amfani da kudaden da za a samar ta hanyoyin da suka dace.
Har ila yau mahukuntan kasar ta Somaliya sun yaba da yadda wakilai mahalarta taron na Brussels suka amince da sharuddan samar da tallafin ginin kasar tsakankanin shekaru 3 masu zuwa.
Taron na wannan karo dai ya samu halartar wakilai daga kimanin kasashe 50, an kuma mai da hankali wajen tattauna muhimman batutuwan da suka shafi zakulo hanyoyin taimakawa kasar ta Somaliya, a kokarinta na shawo kan matsalolin siyasa, da mulki da kuma yanayin zamantakewar al'ummarta. (Saminu)