in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarai na dumi-dumi game da gasar cin kofin duniya
2013-10-10 20:34:14 cri

BRAZIL DA HONDURAS ZA SU BUGA WASAN SADA ZUMUNCI CIKIN WATA MAI ZUWA.

Hukumar gudanar da wasannin kwallon kafar kasar Brazil ta ce yanzu haka an sanya ranar 16 ga watan Nuwamba mai zuwa, a matsayin ranar da kungiyar kwallon kafar kasar ta Brazil za ta kara da takwaransa na Honduras a wani wasan sada zumunci a birnin Miami na kasar Amurka.

Ana dai ganin wannan wasa na sada zumunci da kulaflikan kasashen Biyu zasu buga, tamkar ci gaba ne da share fagen tinkarar gasar cin kofin duniya da kasashen ke yi. Da ma dai tuni kasashen Biyu da ke rukunin kasashen yankin Arewaci da tsakiyar Amurka da Caribbean, suka samu damar shallake shingen wasannin fidda gwani a yankin nasu, wadanda zasu shiga a dama da su a babbar gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil cikin shekarar badi.

Yanzu dai ana sa ran kulaf din dake a matsayi na Hudu a wannan rukuni, ya buga wasan sa na gaba da kasar New Zealand, domin fidda kasa ta karshe a rukunin da za a rankaya da ita gasar cin kofin na duniya daga wannan yanki.

Don gane da gasannin da Brazil zata buga a nan gaba kafin fara waccan gasa ta cin kofin duniya kuwa, hukumar gudanar da wasannin kwallon kafar kasar ta Brazil ta bayyana cewa, akwai wani Karin wasan na sada zumunci guda daya, da kulaf din zai buga da wata kasa wadda ba a bayyana sunan ta ba tukuna, wasan da aka ce za a yi shi ne a ranar 19 ga watan gobe.

Wannan wasa dai zai biyo bayan wasan da Brazil din zata buga da kasar Koriya ta Kudu a birnin Soul a ranar 12 ga watannan na Octoba, sannan wasanta da kasar Zambiya ya biyo baya ran 15 ga watan na Octoba a nan birnin Beijing.

AMURKA TA GAYYACI IRAN WASAN SADA ZUMUNCI

Har yanzu dai muna batun wasannin sada zumunci da manyan kulaflikan kasashe ke shiryawa, inda a nan ma hukumar gudanar da wasannin kwallon kafar kasar Amurka ta mikawa kasar Iran goron gayyatar buga wasan sada zumunci, da ta shirya a kasar ta Amurka.

Jaridar Times Daily dake fita a birnin Tehran ce ta tabbatar da hakan a ranar Asabar 5 ga watan nan na Octoba.

Jaridar ta rawaito shugaban hukumar gudanar da wasannin kwallon kafar kasar ta Iran Ali Kafashian na cewa, hukumarsa ta karbi takardar gayyatar da akai musu, ta halartar wata gasar kulaflika Hudu, wadda hukumar gudanar da wasannin kwallon kafar Amurkan ta shirya domin sada zumunci. Gasar a cewar Kafashian za ta kunshi kasar Iran, da Amurka, da wani kulaf daga nahiyar Turai da wani guda daga Kudancin Amurka.

Dama dai a baya Iran din ta taba buga wasanni guda Biyu da Amurka, inda a shekarar 1998 yayin wasan da kasashen Biyu suka buga a gasar cin kofin duniya na Faransa, Iran ta lashe Amurka da ci 2 da 1. Haka zalika kasahen Biyu sun yi kunnen doki da ci 1 da 1, a birnin Pasadena dake jihar California ta kasar Amurka a shekara ta 2000.

Wannan dai wasa da Iran zata buga da Amurka zai zo ne bayan da kulaflikan kasashen Biyu suka rigaya suka shiga jerin wadanda zasu halarci gasar cin kofin duniya dake tafe badi a kasar Brazil, bayan nasarar da suka samu na tsallake gasar share fagen shiga gasar daga yankunan su. (Zainab/Saminu Alhassan)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China