An ce, ban da filayen wasanni da sauran na'urorin wasanni, kasar Qatar za ta samar da kudin Euro biliyan 110 a shekaru 5 masu zuwa, wajen samarda ababen sufuri, ciki har da jiragen karkashin kasa, filayen jiragen sama, da kuma hanyoyin motoci. Ban da wannan kuma, za a yi amfani da kudin Euro biliyan 15 wajen sha'anin otel-otel.
Gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ta shekarar 2022 da za a gudanar a kasar Qatar, za ta zama karo na farko da za a gudanar da wannan gasa mafi samun karbuwa a fadin duniya a wannan yanki. (Zainab)