131004bagwai.m4a
|
A ranar Laraban nan da ta gabata wao ranar 2 ga wata, Sarkin Kano Alhaji Ado bayero ya dawo gida daga Dubai, inda ya shafe watannin uku yana karbar magani, ya sauka a babban filin jirgin marigayi Malam Aminu Kano jihar Kano da misalin karfe hudu na maraice.
Wakilinmu dake Kano Garba Abdullahi Bagwai ya tattauna da mai ba gwamnan Kano shawara akan harkokin da suka shafi masarautu Alhaji Tijjaniya Mai Lafiya game da yanayin jikin mai martaban da kuma jin ko sarkin zai iya hawan babban sallah mai zuwa?(Garba Abdullahi Bagwai)