in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yau ne Najeriya ke cika shekaru 53 da samun 'yancin kanta
2013-10-01 17:27:48 cri

Yau Talata 1 ga watan Oktoba babbar rana ce mai matukar muhimmanci a tarihin tarayyar Najeriya. Wannan rana ta kasance ranar da kasar ke ciki shekaru 53 da samun 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka. Wakilinmu Murtala dake Najeriya yayi hira da wasu al'ummar kasar don jin ta bakinsu, game da irin ci gaban da Najeriyar ta samu, a cikin wadannan shekaru 53 da suka gabata, tare da jin fatan alherinsu ga makomar kasar. Ga dai wannan rahoto na Murtala.

Yayin da al'ummar Najeriya ke murnar cika shekaru 53 da samun 'yancin kan kasar, batun tsaro na cikin batutuwan dake ci gaba da jan hankali al'umma, tare da janyo ce-ce-ku-ce tsakanin bangarori kasar daban daban. Koda ma a 'yan kwanakin nan, an ji yadda wasu 'yan bindiga suka kaddamar da wasu hare-hare, a wasu yankunan dake jihohin Borno da Yobe, ciki har da harin da aka kaiwa wata kwalejin koyon ilimin gona dake karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe, lamarin da ya haddasa mutuwar dalibai akalla 50.

Yayin zantawar da na yi da wani mazaunin jihar Yobe ta wayar tarho mai suna Alhaji Ali Kiraji Gashua, yace gwamnati tana kara daukar matakan tsaro a wannan lokaci.

A nasa bangare Alhaji Muhammed Yusuf, babban mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin kasuwanci da cinikayya, ya bayyana cewa Najeriya ta samu ci gaba a cikin shekaru 53 da suka gabata, musamman ma a fannin masana'antu da kasuwanci.

Malam Yakubu Ibrahim, wani jami'i ne daga hukumar ilimi ta birnin Abuja, ya bayyana muhimmancin hadin kan kasar ta Najeriya, tare da fatan alherinsa ga kasar a wannan lokaci, na murnar cikarta shekaru 53 da samun 'yancin kai.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China