Sabon tauraron dan Adam din mai lakabin ZA-Cuba, wanda daliban jami'ar Fasaha ta Cape Peninsula suka kera, zai kasance na Uku da kasar za ta mallaka, baya ga Sunsat da Sumbandla da kasar ta harba cikin shekarar 2009.
Da yake karin haske don gane da wannan batu yayin makon bikin nune-nunen fasahohin sararin samaniya na duniya, wanda aka gudanar a garin Kimberley dake lardin Free state, babban daraktan sashen na lura da harkokin Fasahar kasar Phil Mjwara, ya ce tuni aka riga aka kammala aikin hada wannan karamin tauraron dan'adam da daliban jami'ar ta Cape Peninsula suka yi aikin kerawa.
Shi ma a nasa tsokaci yayain bikin, Lorenzo Raynard na cibiyar habaka binciken kimiyya da fasahar kasar ta Afrika ta Kudu, cewa ya yi wannan tauraron dan adam zai taimaka wajen gudanar da ayyukan bincike, tare da baiwa yara 'yan makaranta damar dada fahimtar fannin ilimin kimiyya. Raynard ya ce kammalar wannan muhimmin aiki, na da matukar alfanu ga burin da ake da shi na samarwa 'yan kasar damar shiga a dama da su, a fagen bunkasa ilimin fasahohin sararin samaniya.
Har ila yau aikin ya baiwa kasar damar gudanar da ayyuka da suka dace da wannan biki na makon nune-nunen kayayyakin fasahohin sararin samaniya na duniya. (Saminu)