in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana tsaurara matakan tsaro don kaucewa aukuwar harin ta'addanci a Afirka ta Kudu
2013-10-01 17:45:16 cri
Mahukunta a Afirka ta Kudu na daukar karin matakan tsaron kaucewa aukuwar harin ta'addanci a kasar.

Kakakin ma'aikatar tsaron cikin gidan kasar Brian Dube ne ya bayyana hakan a birnin Pretoria. Dube ya kara da cewa, batun tsaro na cikin batutuwan da dukkanin kasashen duniya ke baiwa kulawa ta musamman.

Wannan dai tsokaci na kakakin ma'aikatar tsaron cikin gidan kasar ta Afirka ta Kudu na zuwa ne bayan da aka bayyana cewa, wata mace 'yar asalin kasar Birtaniya dake dauke da fasfon kasar ta Afirka ta Kudu na cikin wadanda ake zargi da hannu wajen shirya harin ta'addanci da ya sabbaba mutuwar mutane sama da 60, tare da raunata wasu fiye da 170 a kasar Kenya.

Da yake bayyana aniyar kasarsa ta yin hadin gwiwa da sauran kasashe wajen magance ayyukan dake barazana ga harkokin tsaro, Dube ya ce, Afirka ta Kudu a shirye take ta yi tarayya da kasashen dake nahiyar Afirka, dama na wajen nahiyar wajen kakkabe ayyukan ta'addanci, da ma barazanar da suke kawowa ci gaban duniya.

Ko da a ranar Jumma'ar da ta gabata ma dai sai da hukumar 'yan sanda ta duniya INTERPOL ta fid da wata sanarwar dake kunshe da umarni ga mambobinta 190 da su tallafa wajen cafke wannan matar da ake nema ruwa a jallo.

Tun dai ranar Alhamis din da ta gabata ministar harkokin cikin gidan kasar ta Afirka ta Kudu Naledi Pandor ta ce, ma'aikatarta za ta gudanar da bincike kan yadda wadda ake zargin ta samu damar mallakar fasfon kasar Afirka ta Kudu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China