A ranar 19 ga wata, shugaban kasar Jacob Zuma ya bayyana cewa, hadin gwiwar tsakanin kasashen BRICS zai inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasar, da kuma samar da karin guraben aikin yi.
Yayin babban taron horaswa da ilimantar da ma'aikatar matasa ta kasashe renon Ingila da aka kira a Pretoria, babban birnin kasar Afirka ta Kudu, shugaba Jacob Zuma ya nuna cewa, gaba daya, yawan kudin da aka samu wajen samar da kayayyaki na kasashen BRICS ya kai kashi 25 bisa dari na dukkan kasashen duniya, kana kasashen na da yawan mutanen da suka kai kashi 43 bisa dari na duk duniya, yayin da kuma ajiyar kudin musanya da ke wajen wadannan kasasahen BRICS ya kai dallar Amurka biliyan dubu 44.
Bisa wadannan dalilai, hadin gwiwar kasashen BRICS din zai samar da isassun guraben aikin yi ga matasa, da kuma biyan bukatunsu. (Maryam)