Rudunar 'yan sandan kasar Afirka ta Kudu ta bayyana cewa, an riga an tsara wani shirin hadin gwiwa na tabbatar da tsaro yayin da shugabannin kasashen kungiyar BRICS suke ganawa. A halin yanzu, 'yan sanda daga dukkan fadin kasar sun shirya tsaf domin gudanar da aikin tabbatar da tsaro.
Tun daga ranar 26 zuwa ta 27 ga wata ne dai ake sa ran shugabannin kasashen kungiyar ta BRICS za su yi ganawa ta biyar a birnin Durban dake kudu maso gabashin kasar Afirka ta Kudu, inda za su tattauna batun kafa bankin raya kasa, da kara gudanar da ayyukan more rayuwa da dai sauransu. Wannan ne karo na farko da kasar Afirka ta Kudu ta shirya taron kungiyar BRICS tun bayan shigarta kungiyar a watan Disamba na shekarar 2010, kana shi ne karo na farko da aka gudanar da taron a nahiyar Afirka. (Zainab)